An samu arangama tsakanin ’yansanda da masu zanga-zanga a birnin Geneva na ƙasar Switzerland, gabanin fara taron ƙasashen G7 da za a gudanar a Évian-les-Bains na ƙasar Faransa.
Rikicin ya faru ne a wajen hedkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Geneva, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen taron shugabannin ƙasashen G7.
An gudanar da zanga-zangar ne a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar “No-G7”, wadda ta haɗa fiye da ƙungiyoyi 60 da suka haɗa da masu fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawa, masu rajin kare haƙƙin mata da kuma masu kare muhalli.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun jefa kwalabe da duwatsu da kuma gurneti masu ƙara ga jami’an tsaro, yayin da ’yansandan suka mayar da martani da amfani da hayaƙi mai sa hawaye da kuma ruwan zafi domin tarwatsa su.
An kuma ce wasu gine-gine sun lalace sakamakon rikicin, lamarin da ya ƙara nuna tashin hankali a yankin.
Ana sa ran shugabannin ƙasashen G7 za su sauka a filin jirgin saman Geneva kafin su wuce Évian-les-Bains ta hanyar tafkin Geneva domin halartar taron.
Jami’an tsaro sun tsaurara matakan tsaro saboda fargabar sake fuskantar irin zanga-zangar da ta tayar da hankali a lokacin taron G8 da aka gudanar a yankin shekaru 23 da suka gabata.
Haka kuma, babban asibitin Geneva ya fara shirye-shiryen gaggawa, inda aka kafa tantuna na wucin gadi domin kula da duk wanda zai iya jikkata yayin taron ko zanga-zangar.