Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu, bisa zargin gaza cika sharuɗan da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa jam’iyyun ba su samu kaso mafi ƙaranci na ƙuri’un da doka ta tanada a zaɓukan da suka gabata ba.

Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da ADC da Accord da AA da APP da kuma ZLP. Kotun ta ce jam’iyyun sun karya tanade-tanaden sashe na 225 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Haka kuma, kotun ta umarci INEC da kada ta bari jam’iyyun su shiga zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban zaɓen shekarar 2027, har sai sun cika dukkan sharuɗan da doka ta gindaya.

Wata ƙungiyar tsofaffin ’yan majalisa ce ta shigar da ƙarar, tana mai zargin cewa jam’iyyun sun kasa cika ƙa’idojin da suka shafi samun goyon bayan jama’a da kuma sakamakon zaɓe.

Sai dai jam’iyyar ADC ta yi watsi da hukuncin, tare da bayyana cewa za ta ci gaba da shirye-shiryenta na shiga zaɓen 2027, yayin da ta bukaci magoya bayanta da su yi watsi da hukuncin kotun.