Jam'iyyar NDC ta tsayar da Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekarar 2027.
Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya sanar da matakin, inda ya bayyana cewa Mustapha Kwankwaso zai kasance abokin takararsa a zaɓen mai zuwa.
Mustapha Kwankwaso ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano a shekarar 2023, kafin ya ajiye muƙamin a shekarar 2026.
Hadimin Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ne ya tabbatar da wannan mataki ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Rahotanni sun ce an cimma matsayar ne bayan wata ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka gudanar domin tsara dabarun tunkarar zaɓen 2027.