Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da ƙaddamar da wasu zafafan hare-hare kan maɓoyar ’yan bindiga a wasu yankuna na jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rasuwar wani tsohon janar na soja a hannun masu garkuwa da mutane a jihar.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an ƙaddamar da farmakin ne ƙarƙashin wani aiki mai suna Operation Clean Sweep III, domin fatattakar ’yan bindiga daga ƙaramar hukumar Matazu da sauran yankunan jihar Katsina.

Sanarwar ta ce an fara aikin ne tun ranar 14 ga watan Yunin 2026, a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma, wanda ke jagorantar ayyukan soji a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rundunar ta ce ta samu nasarori a yankunan tsaunukan Dikkawa da wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da su, inda aka kai samame a yankunan Adua da Nasarawa da Karaduwa.

A cewar sanarwar, dakarun sojin sun gano tare da lalata maɓoyar ’yan bindiga, wuraren ajiye kayayyaki da sauran cibiyoyin da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

Ta ƙara da cewa an lalata kayayyaki da motocin da ake zargin ’yan bindigar na amfani da su, lamarin da ya rage musu ƙarfin kai hare-hare a yankin.