Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ganowa ta kam tare da gurfanar da mutane da kungiyoyin da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya. tana mai gargadin cewa matsalar tsaro ba za ta kau ba matukar ba a hukunta masu daukar nauyin kungiyoyin masu tayar da kayar baya ba.

Jam’iyyar ta kuma sake jaddada goyon bayanta ga kafa ‘yan sandan jihohi, tana mai cewa tsarin tsaro da aka karkata zuwa matakin jihohi zai karfafa magance matsalar tsaro a yankuna tare da taimakawa wajen magance tabarbarewar tsaro a kasar.

Da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, Shugaban YPP na kasa, Bishop Amakiri, ya soki gwamnatocin da suka gabata bisa gazawarsu wajen magance matsalar tsaro yadda ya kamata. Ya kuma zargi gwamnatin da ke mulki da rashin nuna cikakken kudurin siyasa da ake bukata domin kawo karshen ta’addanci da tada kayar baya.

Amakiri ya nuna damuwa kan ci gaba da yi wa tubabbun ‘yan ta’adda gyaran hali tare da mayar da su cikin al’umma ta hanyar shirin Operation Safe Corridor, alhali kuwa har yanzu akwai dubban wadanda hare-haren ta’addanci suka raba da muhallansu da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a sassan kasar nan.

cewarsa, “Abin da ke ci gaba da bai wa ta’addanci da tada kayar baya karfi a Najeriya shi ne rashin hukunta mutane da kungiyoyin da ke daukar nauyin wadannan laifuffuka.