Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Talata 16 ga Yuni, 2026 a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 bayan hijira.
Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a yau litinin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya al'ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci da ta fara da watan Muharram.
Ya bukaci al'ummar jihar da Musulmi baki daya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani kan ayyukansu na shekarar da ta gabata tare da yin addu'o'in zaman lafiya, hadin kai da ci gaba ga jihar da kasa baki daya.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi inganta rayuwar al'umma ta hanyar shugabanci da ke mayar da hankali kan bukatun jama'a