Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar daga hannun ’yan bindiga bayan wani samame da dakarun haɗin gwiwa suka kai a jihar Katsina.

A wata sanarwa da Daraktan Sashen Yaɗa Labarai na rundunar, Sama’ila Uba, ya fitar, ya ce dakarun Operation Fansan Yamma ne suka gudanar da farmakin a Ƙaramar Hukumar Matazu.

Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun yi arangama da ’yan bindigar a ƙauyen Tunga, lamarin da ya tilasta musu tserewa sakamakon matsin lambar da dakarun suka yi musu.

Sai dai kafin su gudu, ’yan bindigar sun harbi matar marigayin. Duk da haka, sojojin sun yi nasarar ceto ta da rai, inda suka ba ta agajin gaggawa kafin a kai ta asibiti domin ci gaba da kula da lafiyarta.

An yi garkuwa da tsohon kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), tare da matarsa a ranar 30 ga watan Mayun 2026 yayin da suke kan hanyarsu daga Marabar Musawa zuwa Kafinsoli a jihar Katsina.

A ranar 13 ga watan Yuni, gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rasuwar tsohon janar ɗin a hannun masu garkuwa da mutanen, inda ta danganta mutuwarsa da matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon suga da hawan jini.

Hukumomin soji sun ce suna ci gaba da farautar sauran ’yan bindigar da suka tsere domin gurfanar da su a gaban shari’a.