Aƙalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu bayan da mayaƙan ƙungiyar Lakurawa suka kai hari ƙauyen Fasken Rafi da ke ƙaramar hukumar Arewa a jihar Kebbi.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne a ranar Lahadi, inda mazauna yankin suka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin hare-haren da aka tsara sosai da aka kai kan al’umma a kwanakin baya-bayan nan. Harin ya kuma jikkata wasu mutane da ke karɓar magani a cibiyoyin lafiya da ke kusa.

Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta tura wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar, Umar Tafida, domin jajanta wa iyalan waɗanda harin ya shafa tare da tantance halin da ake ciki.

Yayin ziyarar, Tafida ya yi Allah-wadai da harin, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce gwamnati za ta tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki zuwa yankin domin dakile irin waɗannan hare-hare a nan gaba.

Harin ya sake ƙara nuna damuwar da ake yi kan matsalar tsaro a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda al’ummomi ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƙungiyoyin ’yan bindiga da mayaƙan Lakurawa.

Lamarin ya zo ne kwanaki bayan Sarkin Argungu, Alhaji Mohammed Mera, ya yi kira ga al’ummomi da su ɗauki matakan kariya da suka dace da doka domin kare kansu daga hare-haren masu tayar da ƙayar baya.