Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya yi zargin cewa an yi amfani da sa hannun jabu ko kuma aka saka sunayen wasu sanatoci ba tare da amincewarsu ba a rahoton da ya ba da shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na AIT, inda ya ce akalla sanatoci uku sun shaida masa cewa ba su sanya hannu a rahoton ba duk da cewa an saka sunayensu a ciki.
Ya ce Sanatar Babban Birnin Tarayya (FCT), Ireti Kingibe, na daga cikin wadanda suka ce ba su sanya hannu a rahoton ba, amma an wallafa sunanta a matsayin mai amincewa da shi.
Tsohon gwamnan jihar Edo ya jaddada cewa sanya sunan dan majalisa a rahoto ba tare da amincewarsa ba ya saba ka’idojin majalisa, domin sanya hannu na nufin amincewa da abin da rahoton ya kunsa.
Rahoton da ake magana a kai shi ne wanda Kwamitin Da’a, Hakkoki da Korafe-korafen Jama’a na Majalisar Dattawa ya gabatar, wanda ya kai ga dakatar da Sanata Natasha a watan Maris na 2025 bisa zargin rashin da’a da karya dokokin majalisa.
Dakatarwar ta haddasa ce-ce-ku-ce musamman saboda rikicin da ya barke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio. Sai dai majalisar ta dage cewa matakin da aka dauka ya danganci halayyarta a zaman majalisa ne kawai.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, shugabannin Majalisar Dattawa da kwamitin da ya gabatar da rahoton ba su fitar da wata sanarwa kan zargin da Oshiomhole ya yi ba.