Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani babban kwamitin da zai gudanar da bincike kan satar gyadar tamowa abincin yara mai suna RUTF.da aka tanada domin kula da yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a faɗin jihar.
Yayin ƙaddamar da kwamitin a madadin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin gano haƙiƙanin abin da ya faru na zargin karkatar da waɗannan muhimman kayayyakin ceto rayuka, tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
Wannan na kunshene cikin wata sanarwa mau dauke da sa hannun mai Magana da yawun ma’aikatar lafiya ta jihar kano Nabilisi Abubakar Kofar na’isa
Cikin sanarwar, Kwamishinan lafiya Dr abubakar labaran yusuf, ya ce ana sa ran kwamitin zai bayar da shawarwari kan matakan gudanarwa, ladabtarwa da gyara da ya kamata a ɗauka, tare da gabatar da ƙarin shawarwari idan akwai buƙata, sannan ya miƙa rahotonsa cikin kwanaki goma sha huɗu daga ranar ƙaddamar da shi.
A cewar sa Gwamnatin Jihar Kano ta kashe sama da Naira miliyan 500 wajen sayo kayayyakin RUTF domin tallafa wa yara dake fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki marasa galihu.
Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Pharm. Aminu Bashir, ne zai jagorantar kwamitin, wanda ya ƙunshi mambobi goma sha takwas daga sassa daban-daban masu ruwa da tsaki, ciki har da jami’an tsaro, wakilan Majalisar Masarautu, Kwamitocin Raya Unguwanni daga yankunan Dawakin Tofa, Wudil, Rano da Bichi, da sauransu. Daraktan Gudanarwa da Harkokin Ma’aikata na Ma’aikatar, Alhaji Naziru Tanko Kyaure, zai kasance Sakataren kwamitin.
Da yake jawabi a madadin kwamitin, Shugaban Kwamitin, Pharm. Aminu Bashir, ya tabbatar wa Gwamnatin Jihar Kano da al’ummar jihar cewa za su gudanar da aikin da aka ɗora musu cikin ƙwarewa, gaskiya da rikon amana har sai an gano gaskiyar lamarin.