Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya sanar da sabbin matakan tsaro domin daƙile ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.


A cikin umarnin da ya fitar bayan taron gaggawa na tsaro, gwamnatin ta haramta saye, sayarwa, jigilar kaya da adana man fetur a cikin jarkoki a faɗin jihar baki ɗaya.


Haka kuma, an rufe dukkan cibiyoyin POS da wuraren cajin wayoyi na kasuwanci a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa, bayan rahotannin tsaro sun nuna cewa masu laifi na amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.


Bugu da ƙari, gwamnatin ta hana amfani da babura a duk faɗin ƙananan hukumomin Matazu da Musawa domin dakile zirga-zirgar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane waɗanda galibi ke amfani da babura wajen kai hare-hare.


Gwamna Radda ya ce matakan na da nufin katse hanyoyin sadarwa da samar da kayan aiki ga masu aikata laifuka, tare da tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya kuma yi kira ga mazauna jihar su bi umarnin tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai, yana mai gargaɗin cewa za a hukunta duk wanda ya karya sabbin dokokin.