Rundunar ’Yan Sandan Jihar Plateau ta tabbatar da mutuwar jami’an tsaro uku a wata matsalar tsaro da ta faru a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a Jos da sanyin safiyar ranar Talata.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Alfred Alabo, ya fitar, ya ce lamarin ya shafi wasu jami’an tsaro da ke bakin aiki a cibiyar a lokacin da abin ya faru.

Alabo ya bayyana cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Plateau, CP Bassey Ewah, ya tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin tare da ƙarfafa sintiri domin tabbatar da tsaron mazauna yankin da kuma hana sake afkuwar makamancin wannan matsala.

Rundunar ta ce an shawo kan lamarin kuma harkokin yau da kullum sun koma yadda suke a cikin cibiyar da ma yankunan da ke kewaye da ita.

Sanarwar ta ƙara da cewa an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin da kuma tantance cikakken abin da ya faru.

Rundunar ’yan sandan ta kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.