Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta fitar da sakamakon jarabawar UTME ta maimaitawa, wadda aka gudanar ga ɗaliban da ba su samu damar rubuta jarabawar farko ba, saboda matsalolin fasaha da tantance bayanan halittu (biometric verification).
A cikin sanarwar da Mai Ba da Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai na Hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ya fitar, ya buƙaci ɗaliban da abin ya shafa su duba sakamakonsu ta hanyoyin da hukumar ta amince da su.
Dakta Benjamin ya bayyana cewa, bayan fitar da sakamakon, hukumar za ta fara tantancewa da tsara jerin ɗalibai bisa ga maki da suka samu, wanda ke zama wani muhimmin mataki a tsarin bayar da guraben karatu a manyan makarantu.
Sanarwar ta kuma yaba wa ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki saboda haƙuri da fahimtar da suka nuna yayin gudanar da wannan tsari.
Haka kuma, hukumar ta ce ana sa ran fara buga takardun sakamakon da ɗalibai za su yi amfani da su wajen neman guraben karatu kafin ƙarshen wannan mako