Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana Kamfanin Nigeria LNG (NLNG) a matsayin wata muhimmiyar kadara ta ƙasa, tana mai cewa nasarorin da kamfanin ke samu sun yi daidai da manufofin gwamnati na tabbatar da tsaron makamashi da jawo hannun jari da bunƙasa masana’antu.
Ministar ta bayyana hakan ne lokacin da ta karɓi bakuncin Manajan Daraktan NLNG, Injiniya Adeleye Falade, a Abuja.
A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun amince da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin bunƙasa diflomasiyyar tattalin arzikin Najeriya da kuma jawo ƙarin zuba jari a fannin makamashi.
Shi ma Manajan Daraktan NLNG ya taya ministar murna kan naɗinta, yana mai bayyana cewa kamfanin na taka muhimmiyar rawa wajen tallata damar tattalin arzikin Najeriya a idon duniya.
Falade ya yi bayani kan aikin Train 7 Project, wanda zai ƙara yawan iskar gas da kamfanin ke samarwa daga tan miliyan 22 zuwa tan miliyan 30 a shekara, tare da samar da ƙarin ayyukan yi da kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Bianca Odumegwu-Ojukwu ta nuna jin daɗinta game da ƙarin haɗin gwiwar, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen jawo muhimman masu zuba jari da kuma nuna damarmakin da ke akwai a fannin makamashin Najeriya.
Dukkan ɓangarorin sun sake jaddada aniyarsu ta zurfafa haɗin gwiwa domin ƙara ƙarfin Najeriya a fagen gasa na duniya da kuma ƙarfafa matsayin ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da suka fi jan hankalin masu zuba jari a nahiyar Afirka.
A halin yanzu, NLNG na samar da dubban ayyukan yi tare da bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin ƙasa ta hanyar haraji da rabon riba da kuma bunƙasa amfani da ƙwararrun cikin gida.