Majalisar Dattawa ta yi watsi da zargin da Sanata Adams Oshiomhole ya yi cewa an ƙirƙira sa hannun bogi na wasu sanatoci ba bisa ka’ida ba a cikin rahoton da ya ba da shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, tana mai bayyana zargin a matsayin marar tushe.


Jarida punch ta rawaito cewa, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, a yayin wata tattaunawa da Wakilinnsu ya ce matakin ladabtarwa da aka ɗauka kan sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ya bi dukkan matakan doka da ka’idojin majalisar, kuma an gudanar da shi a fili a zauren majalisar.


Adaramodu ya ce Majalisar Dattawa ta riga ta tabbatar da cewa duk wani ɗan majalisar da ya karya dokokinta zai fuskanci hukunci, yana mai jaddada cewa batun da ya shafi Akpoti-Uduaghan an tattauna shi a bainar jama’a.


Ya ce, “An ladabtar da Sanata Natasha ne saboda karya dokokin Majalisar Dattawa. Mun bayyana karara cewa duk wanda ya kasa bin dokokin majalisar zai fuskanci sakamako.


“An gabatar da batun a fili yayin zaman majalisar. ‘Yan jarida suna wurin, kowa ma yana wurin, kuma an gudanar da dukkan shari’ar a bude. Daga bisani kuma an miƙa batun ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Da’a da karbar Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a.”