Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ɗaukar ma’aikatan tsaron gandun daji (Forest Guards) guda 1,000 domin ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar tsaro a Jihar Katsina.
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawa da malamai na addinin Musulunci da sauran masu ruwa da tsaki a Gidan Gwamnati da ke Katsina.
Taron ya ba da damar tattaunawa kan hanyoyin da al’umma za su taka rawa wajen magance matsalolin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.
Radda ya ce ganawar da aka yi da shugabannin addini na da nufin fahimtar musabbabin rikicin tsaro da kuma samun shawarwari kan hanyoyin warware matsalar cikin ɗorewa, baya ga hanyoyin soji da aka saba amfani da su.