Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar sun ƙara wa jihohi kuɗaɗen shiga domin gudanar da ayyukan raya ƙasa.


Onanuga ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Umuahia, babban birnin Jihar Abia, yayin wani taron karɓar baƙuncin tawagar yawon duba ayyukan gwamnatin tarayya Karkashin shirin Renewed Hope ta kafafen yaɗa labarai, wadda ta kai ziyara jihar domin duba ayyuka daban-daban da aka aiwatar tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da kuma waɗanda gwamnatin jihar ta gudanar.


A cikin jawabinsa, Onanuga ya ce wannan yawon duba ayyuka zai bai wa mahalarta damar tantance manyan ayyukan gwamnatin tarayya da na jihohi cikin adalci da gaskiya, tare da ganin irin ci gaban da ake samu a sassan ƙasar nan.


Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi wajen ciyar da ƙasa gaba, tare da yabawa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin su.


Ya ce, “Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi na aiki tare domin ci gaban ‘yan Najeriya. Albarkatun da jihohi ke samu a yanzu suna ba su damar aiwatar da ayyukan da ke inganta rayuwar al’umma.”


A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, wanda Mataimakin Gwamnan jihar, Ikechukwu Emetu, ya wakilta, ya bayyana ziyarar a matsayin wani muhimmin mataki na inganta gaskiya, rikon amana da kuma wayar da kan jama’a game da ayyuka da manufofin gwamnati a faɗin ƙasar.


Otti ya lura cewa al’umma na dogaro da kafafen yaɗa labarai wajen samun sahihan bayanai, don haka ya ce akwai buƙatar tawagar ta yi fiye da bayar da rahoton abubuwan da suka faru kawai, ta kuma samar da cikakken bayani, daidaito da gaskiya a rahotannin da take gabatarwa.