Hukumar Kwastam ta Najeriya ta yi karin haske kan zargin rashin miƙa Naira biliyan 62.2 ga Asusun Tarayya, yayin wani zaman bincike da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Asusun Jama'a ya gudanar.

Hukumar ta bayyana cewa kuɗaɗen da aka bayyana a matsayin waɗanda ba a miƙa ba a shekarar 2017, harajai ne da ta karɓa a madadin wasu hukumomi, kuma ba kuɗaɗen da ya kamata a tura kai tsaye zuwa Asusun Tarayya ba ne.

Bayanin ya zo ne a matsayin martani ga tambayar bincike da Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya ya gabatar, wadda ta samo asali tun daga shekarar 2019.

Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana cewa yawancin harajan da hukumar ke tattarawa ana miƙa su ga Asusun Tarayya, sai dai wasu kuɗaɗe da suka shafi kayayyakin da ake samarwa a cikin gida kamar alkama da masaku da giya, waɗanda ke da tsarin gudanarwa na musamman.

A cewarsa, hukumar za ta gana da wani ƙaramin kwamitin da aka kafa domin daidaita dukkan batutuwan da aka samu kuskure wajen rubuta su a cikin rahoton binciken kuɗaɗen.