Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi kira da a ɗauki matakan kariya na gaggawa domin ƙarfafa tsaron iyakokin Najeriya daga laifuffukan ƙetare da kuma sabbin barazanar tsaro da ke tasowa.
Da yake jawabi a wani taron ƙasa na wuni guda mai taken “Tsaron Iyakoki, Haɗin Gwiwar kasahen Ƙetare ” wanda Hukumar Kula da Iyakokin Ƙasa (NBC) ta shirya, Musa ya ce wajibi ne Najeriya ta sauya tsofaffin hanyoyin tsaro ta rungumi zamani , da fasahar gargaɗin Kai tsaye da fasaha ke jagoranta, da kuma ƙarfafa musayar bayanan sirri da ƙasashen maƙwabta.
Ya bayyana cewa ingantaccen kula da iyakoki yana da matuƙar muhimmanci ga tsaron ƙasa da bunƙasar tattalin arziki.
Musa ya ce iyakokin Najeriya ba wai kawai layukan raba ƙasa ba ne, wurare ne masu muhimmanci na kasuwanci, mu’amalar zamantakewa da kuma gadon al’adu na bai ɗaya.
Sai dai ya lura cewa iyakokin na kuma kasancewa sahun gaba wajen yaƙi da fasa ƙwauri, tafiye - tafiye ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifuffukan ƙetare ƙasa.
Ya ce, “Iyakokin kasa masu nagarta da Aminci, ba wai waɗanda aka tsare kawai ba ne, su ne waɗanda suke iya daidaitawa da sauye-sauye, masu haɗa kowa da kowa, kuma masu iya jurewa barazanar tsaro, sauyin yanayi da kuma matsalolin tattalin arziki.”
Tun da farko, Darakta Janar na NBC, Surv. Adamu Adaji, ya ce tabbatar da tsaron iyakokin Najeriya na buƙatar haɗin gwiwar kowa da kowa.
Ya bayyana cewa Najeriya tana da kusan kilomita 4,454 na iyakokin ƙasa da ƙasashen Benin, Nijar, Chadi da Kamaru, baya ga gabar tekun da ta kai kilomita 853.
Adaji ya ce hukumar ta kafa dandamalin haɗin gwiwar ƙetare iyaka da ya haɗa al’ummomin kan iyaka, sarakunan gargajiya, hukumomin tsaro da ƙungiyoyin farar hula domin inganta tattaunawa, tattara bayanan sirri da kuma hana rikice-rikice.
Kwamandan Kwalejin Tsaro ta Ƙasa (National Defence College), Rear Admiral Abdullahi Ahmed, ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya magance ƙalubalen iyakoki yadda ya kamata ita kaɗai, yana mai kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen yankin.
Hakiman gargajiya daga yankunan kan iyaka, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Machina, Alhaji (Dr.) Bashir, sun buƙaci gwamnati ta ƙara bai wa cibiyoyin gargajiya muhimmiyar rawa wajen daidaita harkokin tsaro, suna masu bayyana su a matsayin “ido da kunne na farko” na al’ummomin da ke kan iyaka.