Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba da tallafin naira miliyan 100 ga ƙananan ’yan kasuwa mata 2,000 a Jihar Benue domin su fara ko kuma su bunƙasa harkokinsu na kasuwanci.
Ta bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da Cibiyar Yaɗa Bayanai da Fasahar Sadarwa ta Al’umma (ICT) da ke Ihugh, a Ƙaramar Hukumar Vandeikya ta jihar, inda ta jaddada cewa fasahar ICT muhimmiyar hanya ce ta ƙarfafa al’umma, musamman mata.
Remi Tinubu ta ce a yanzu Benue tana da cibiyoyin ICT guda huɗu, yayin da aka kafa wasu guda 15 a jihohin tarayya da suka haɗa da Abia, Cross River, Rivers, Delta, Ebonyi, Edo, Jigawa da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ta bayyana cewa an tanadi kwamfutoci da sauran kayan aikin ICT a dukkan cibiyoyin, tare da ƙara da cewa an ƙaddamar da shirin ne domin rage gibin fasahar zamani da ke tsakanin al’ummomin ƙasar.
Ta ce: “Sanin fasahar ICT muhimmiyar hanya ce ta ƙarfafa al’umma, musamman mata, kuma zai ba su damar samun sabbin damammaki tare da taimaka wa matasa wajen bunƙasa iliminsu domin shiga tattalin arzikin duniya.
“Game da tallafin kuwa, shirin Renewed Hope Initiative zai bayar da tallafin naira miliyan 50 ga mata 1,000 a Vandeikya, sannan kuma ƙarin naira miliyan 50 ga wasu mata 1,000 a Makurdi da kewaye domin ƙara jari a kasuwancinsu da suke yi a yanzu. Hakan ya kai jimillar naira miliyan 100 da za a yi amfani da ita wajen ƙarfafa mata 2,000 masu sana’o’in ƙananan kasuwanci.”