Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sanya fitilun solar a makarantun Tsangaya da ke mazabu 361 na jihar domin inganta yanayin koyarwa da karatu.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, inda ya bayyana cewa Majalisar Zartarwar Jihar Katsina ta amince da samar da fitilun solar 30 a makarantun Tsangaya da ke kowace mazaba a fadin jihar.


Sanarwar ta ce shirin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na inganta harkar ilimi tare da samar da ingantaccen yanayi ga daliban makarantun Tsangaya.


Mai Bai Wa Gwamnan Shawara Kan Wutar Lantarki da Makamashi, Dakta Hafiz Ahmed, ya bayyana cewa sanya fitilun solar din zai taimaka wajen inganta karatu musamman a lokutan dare, tare da kara matakan tsaro a harabar makarantun.


Ya ce samar da hasken lantarki mai dorewa zai ba dalibai damar ci gaba da gudanar da karatunsu cikin sauki da kwanciyar hankali.


A wani bangare kuma, Majalisar Zartarwar Jihar Katsina ta amince da aiwatar da tsarin kasafin kudi da ya shafi sauyin yanayi a ma’aikatun gwamnati da kananan hukumomin jihar.


Gwamnatin ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen karfafa manufofin kare muhalli, rage illolin sauyin yanayi da kuma bunkasa ci gaba mai dorewa a fadin jihar.