Ƙungiyar masu gidajen mai ta Nijeriya (PETROAN) ta bayyana cewa rage farashin man fetur da matatar Dangote ke yi ba ya bayyana kai tsaye a gidajen mai saboda wasu dalilai da suka shafi samarwa da rarraba man fetur.

Shugaban ƙungiyar, Billy Gillis-Harry, ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce farashin man fetur ga masu amfani da shi na dogara ne da abubuwa da dama, ciki har da wadatar man a wurare daban-daban, kuɗin jigila, ajiya da kuma yadda ake kai man zuwa gidajen mai.

Ya ce idan farashin man ya ƙaru, masu gidajen mai kan ɗaga farashi cikin gaggawa domin samun damar sake sayen sabon kaya da sabon farashin. Sai dai idan farashin ya ragu, galibi sai an fara sayar da tsohon man da aka saya da tsada kafin a fara ganin tasirin sabon ragin.

Wani masanin harkokin makamashi, Olabode Sowunmi, ya ce duk da cewa farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya na da tasiri, ba shi ne babban abin da ke ƙayyade farashin man fetur a Nijeriya ba.

A cewarsa, tsarin da matatar Dangote ke amfani da shi wajen sayen wani kaso na ɗanyen mai da kuɗin naira yana rage tasirin canje-canje a farashin mai na duniya kan kasuwar cikin gida.

Ya ƙara da cewa babban ƙalubalen da ke hana masu amfani ganin saukar farashin kai tsaye shi ne tsadar jigila da kuma tsarin rarraba man daga matatar zuwa gidajen mai a sassan ƙasar.

A makonnin baya, matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N1,275 zuwa N1,250 kan kowace lita, yayin da ta rage farashin dizal daga N1,800 zuwa N1,700 kan kowace lita.

Kamfanin ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na rage wa jama'a da 'yan kasuwa nauyin tsadar makamashi tare da ƙara inganta wadatar man fetur a faɗin ƙasar.

Sai dai duk da wannan ragi, PETROAN ta ce masu amfani da man fetur na iya jira na ɗan lokaci kafin su fara ganin cikakken tasirin saukar farashin a gidajen mai saboda dalilan kasuwanci da na tsarin rarrabawa.