Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa rashin cikakken tsaro a kan iyakokin Najeriya na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa matsalolin tsaro a ƙasar.
Ribadu ya ce matsalolin sun haɗa da ta’addanci, safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, fasa kwauri, safarar mutane da kuma ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin buɗe taron ƙara wa juna sani na ƙasa karo na 15 kan harkokin tsaro, wanda Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Tsaron Ƙasa (AANDEC) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Kwalejin Tsaron Ƙasa (NDC).
A cewarsa, akwai buƙatar gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara ɗaukar matakai masu ƙarfi wajen kula da iyakokin ƙasar domin dakile shigowa da makamai ba bisa ƙa’ida ba, tare da hana ayyukan ƙungiyoyin ta’addanci da sauran masu aikata laifuka.
Ya jaddada cewa inganta tsaro a kan iyakoki na da matuƙar muhimmanci wajen rage barazanar tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.