Kwamitin Raba Kudaden Tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.3 ga matakan gwamnati uku a matsayin rabon kudaden shiga na watan Mayun 2026.

Adadin da aka amince da shi a taron FAAC na watan Yunin 2026 ya kunshi Naira tiriliyan 1.611 daga kudaden shiga na doka (Statutory Revenue) da kuma Naira biliyan 688.785 daga harajin ƙarin darajar kaya da ayyuka (VAT).

Daga cikin kudaden da aka raba, Gwamnatin Tarayya ta karɓi Naira biliyan 818.680, yayin da gwamnatocin jihohi suka samu Naira biliyan 759.141. Haka kuma, kananan hukumomi sun karɓi Naira biliyan 534.277.

Jihohin da ake hako mai kuwa sun samu ƙarin Naira biliyan 188.132 a matsayin kaso na kashi 13 cikin 100 na kuɗaɗen haƙar mai (derivation).

Kwamitin ya bayyana cewa jimillar kudaden shiga na doka da aka tara a watan Mayu ta kai Naira tiriliyan 2.652, wanda ya nuna karin Naira biliyan 273.623 idan aka kwatanta da watan Afrilu.

A cewar FAAC, karin kudaden ya samo asali ne daga karuwar kudaden harajin kamfanoni (CIT), harajin ribar kadarori (CGT), harajin tambura (Stamp Duties), harajin ribar man fetur (PPT), harajin Hydrocarbon da kuma kudaden sarautar mai (Oil Royalties).

Sai dai kudaden VAT sun ragu zuwa Naira biliyan 743.668 a watan Mayu daga Naira biliyan 806.617 da aka samu a watan Afrilu.

Duk da wannan ragin, FAAC ta ce karin kudaden da aka samu daga harajin da suka shafi man fetur da kuma harajin kamfanoni sun taimaka wajen ƙarfafa yawan kudaden shiga da aka samu a watan Mayun 2026.