Gabanin zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), Najeriya ta sanya hannu kan wata sabuwar takardar jaddada goyon baya ga Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ajandar gyaran tsarin MDD ta UN80.
Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ne ya sanya hannu a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
Jakada Ibrahim, wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi, Kashe-Kashe da Gudanarwa na MDD, ya ce matakin ya nuna cikakken amincewar Najeriya da makomar Majalisar Ɗinkin Duniya da muhimmancin haɗin gwiwar ƙasashen duniya.
A wani taro da ya gudana a gefe, wakilin Najeriya ya karɓi Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, a gidan ofishin jakadancin Najeriya da ke New York.
A yayin ganawar, an yi mata bayani kan manufofi da dabarun da Najeriya ke bi a cikin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da sake jaddada aniyar ofishin jakadancin na yin aiki kafada da kafada da shugabannin MDD.
Haka kuma, bangarorin sun tattauna kan aiwatar da wani shirin aiki na kwanaki 90 da ke da nufin ƙarfafa murya da tasirin Najeriya a harkokin duniya.