Wata kotu a birnin Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗauri da tarar kuɗi bayan an same shi da laifin tara buhunan ba-haya a ƙofar gidansa, lamarin da ya haddasa mummunan wari tare da barazana ga lafiyar maƙwabtansa.

An gurfanar da Mohammed Sa’idu ne bayan mazauna unguwar sun kai ƙorafi kotu, suna zargin cewa buhunan ba-hayar da yake jibgawa a ƙofar gidansa sun jawo wari mai tsanani wanda ya hana su walwala da zama cikin kwanciyar hankali.

Mai shari’a Halima Wali ta yanke hukuncin ɗaurin wata huɗu tare da tarar Naira 100,000, tana mai bayyana abin da ya aikata a matsayin barazana ga lafiyar jama’a da muhallin maƙwabta.

Sa’idu, wanda ke sana’ar tara da sayar da ba-haya ga manoma domin amfani da shi a matsayin taki, ya amsa laifinsa a gaban kotu tare da amincewa cewa aikinsa ya jefa rayuwar mutane cikin haɗari.

Kafin yanke hukuncin, mai shari’ar ta kai ziyara da kanta zuwa wurin domin tabbatar da ƙorafin da aka gabatar, inda ta ga tarin buhunan ba-hayar da aka ajiye a ƙofar gidan.

Kotun ta kuma umarci Sa’idu da ya kwashe dukkan buhunan ba-hayar daga wurin tare da ɗaukar alƙawarin cewa ba zai sake aikata irin wannan abu ba.

Ɗaya daga cikin masu ƙorafin, Malam Samaila Inuwa, ya ce sun yi ƙoƙarin warware matsalar cikin lumana amma Sa’idu ya ƙi daina tara ba-hayar a wurin.

Shi ma Mai Unguwar yankin, Musa Abdullahi, ya ce tun farko ya yi masa gargaɗi kan lamarin, amma daga bisani ya sake komawa kan aikinsa, abin da ya sa maƙwabta suka yanke shawarar kai ƙara kotu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa rayuwarsu ta inganta tun bayan da kotu ta shiga lamarin, inda suka ce yanzu suna zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da mummunan wari ba.