Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta haramta wa ma’aikatan gwamnati da na hukumomin tsaro zuwa wuraren aiki da manyan wayoyi, a wani sabon mataki da ta ce an ɗauka domin ƙara mayar da hankali kan ayyukan gwamnati.
Ma’aikatan gwamnati da dama sun shaida wa BBC cewa an umarce su da kada su kawo wayoyin hannu na zamani zuwa ofisoshi da wuraren aiki, yayin da wasu suka ce an gargade su da su rage amfani da wayoyin har ma a gidajensu.
Wani jami’in gwamnatin Taliban ya bayyana cewa manufar matakin ita ce tabbatar da cewa ma’aikata suna mayar da hankali kan ayyukan da aka ɗora musu maimakon ɓata lokaci wajen amfani da wayoyi.
Sai dai masu sa ido kan harkokin siyasa da tsaro suna ganin matakin na iya kasancewa wani yunkuri na Taliban na ƙara tsaurara iko kan bayanai da sadarwa, tare da hana fitar da muhimman bayanai daga cibiyoyin gwamnati.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa an ji wani ɗan Taliban a cikin wani saƙon murya yana gargadin wani ma’aikacin gwamnati cewa duk wanda aka samu da karya dokar zai fuskanci hukunci a gaban kotun sojoji.
Matakin na daga cikin jerin dokoki da gwamnatin Taliban ke aiwatarwa domin ƙara tsaurara tsarin gudanarwa da kula da ayyukan gwamnati tun bayan komawarta kan mulki a Afghanistan.