Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, ya bayyana cewa kowace ƙasa na da haƙƙin kare kanta, amma ya jaddada cewa Isra'ila dole ne ta mutunta yarjejeniyoyin zaman lafiya da ake ƙoƙarin cimma a yankin Gabas ta Tsakiya.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan sukar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi game da hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon, Vance ya ce ba ya son tauye wa Isra'ila haƙƙinta na kare kanta daga barazanar tsaro.
Duk da haka, ya bayyana damuwarsa game da wani hari da ya afku a wani yanki da jama'a ke zaune a birnin Beirut, yana mai cewa abin ya faru ne a daidai lokacin da ake kusa da cimma muhimmiyar yarjejeniyar zaman lafiya.
"Da alama muna gab da samun gagarumar nasara wajen cimma yarjejeniya, sai kuma aka samu wani babban fashewa a wani yanki da jama'a ke zaune a Beirut. Wannan abu ne da ba za a yarda da shi ba," in ji Vance.
Ya kuma ce Amurka na son ci gaba da haɗin gwiwa da Isra'ila domin samar da wani tsari mai ɗorewa na tsaro da zaman lafiya a yankin.
A cewarsa, wannan haɗin gwiwar zai taimaka wajen katse hanyoyin samun kuɗi na ƙungiyar Hezbollah tare da hana ta kai hare-hare kan Isra'ila, abin da zai ƙara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.