Firaministan ƙasar Equatorial Guinea, Manuel Osa Nsue Nsua, ya yi murabus tare da dukkan mambobin gwamnatinsa bayan zargin cewa sun gaza cika alƙawuran da aka ɗora musu.

Mataimakin Shugaban Ƙasar, Teodoro Nguema Obiang Mangue, wanda shi ne ɗa ga Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya bayyana cewa gwamnatin ta kasa cimma har ma da kashi 10 cikin 100 na manufofin da aka ɗora mata tun lokacin da aka kafa ta.

Ya ce firaministan ya miƙa takardar murabus ɗinsa tare da sauran ministoci da manyan jami’an gwamnati, bayan an yi nazari kan yadda suka gudanar da ayyukansu.

Ko da yake ba a bayyana takamaiman manufofin da aka gaza ba, sanarwar da jam’iyyar gwamnati ta PDGE ta fitar ta ce shugaban ƙasar ya nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin ta yi yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ƙoƙarin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Jam’iyyar ta ce gwamnatin ta gaza samar da ci gaba mai gamsarwa duk da albarkatun man fetur da ƙasar ke da su.

Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, wanda ya fara mulkin ƙasar tun shekarar 1979 kuma ake kallonsa a matsayin shugaban ƙasa mafi dadewa a duniya, shi ne ya naɗa gwamnatin da ta yi murabus a shekarar 2024 tare da Manuel Osa Nsue Nsua a matsayin firaminista.

PDGE ta ƙara da cewa shugaban ƙasar bai gamsu da yadda gwamnatin ta gudanar da ayyukanta ba, kuma ana sa ran zai naɗa sabuwar gwamnati nan da nan.