An kashe sojoji 11 a harin da aka kai filin jirgin sama na birnin Niamey a Jamhuriyar Nijar, inda aka ce an kashe mutane 30 gabaɗaya.
Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta ce daga cikin mutanen da aka kashe akwai sojoji 11 da fararen hula biyu, yayin da aka kashe mutum 22 daga cikin maharan.
Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka fara jin ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a babban filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na birnin Niamey. Har yanzu ba a bayyana waɗanda suka kai harin ba.
Hukumomin ƙasar sun ce an daƙile harin, kuma za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a filin.
Nijar tare da maƙotanta Mali da Burkina Faso na ci gaba da fuskantar ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga a yankin.