Tsoffin hafsoshin sojin Najeriya da abokan aikin marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su sake duba tsarin tsaron ƙasar tare da ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar rashin tsaro.

Sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, bayan rasuwar tsohon Janar ɗin wanda aka ce wasu ƴan bindiga sun sace tare da kashe shi a Jihar Katsina.

Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (mai ritaya), wanda ya yi magana a madadin abokan aiki da iyalan marigayin, ya ce lokaci ya yi da za a yi wa tsarin tsaron ƙasar garambawul domin dakile ayyukan ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

A nasa jawabin, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), tsohon Darakta Janar na Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), ya bukaci gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce akwai buƙatar samar da sabbin dabaru da za su taimaka wajen wargaza ƙungiyoyin ƴan bindiga da na ta’addanci tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

“Waɗannan mutane ƴan adam ne kamar mu. Suna tsoron mutuwa kuma suna tsoron a tunkare su kai tsaye. Idan muka kawar da tsoro daga zukatanmu kuma muka fuskance su da ƙwazo, za mu samu sakamako mai kyau fiye da ci gaba da tattaunawar da ba ta da iyaka,” in ji Tsiga.

Ya kuma bayyana cewa bisa gogewarsa da lokacin da ya shafe a hannun masu garkuwa da mutane, yana da wuya ƙungiyoyin ƴan bindiga da na ta’addanci su ajiye makamansu ko su miƙa wuya ta hanyar tattaunawa kawai.

Tsoffin hafsoshin sun jaddada cewa akwai buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da al’umma domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.