Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba ta da niyyar janye sojojin Isra’ila daga kudancin Lebanon da kuma yankunan da take kallon su a matsayin shingen kariyar tsaro.

Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin da wasu mambobin majalisarsa ke ci gaba da sukar yarjejeniyar da ake ƙoƙarin cimmawa tsakanin Amurka da Iran.

Ya ce kamar yadda Isra’ila ta samu nasarar dawo da tsaro da zaman lafiya a yankunan da ke kan iyaka da Zirin Gaza, haka kuma tana da burin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a birane da ƙauyukan arewacin ƙasar.

“Kiyaye tsaron al’ummomin da ke arewacin Isra’ila na buƙatar ci gaba da kasancewar yankin kariyar tsaro a kudancin Lebanon. Saboda haka, ba za mu janye daga wuraren ba muddin tsaron Isra’ila na buƙatar hakan,” in ji Netanyahu.

A wani ɓangare kuma, Iran ta nuna goyon baya ga wasu tanade-tanaden yarjejeniyar fahimtar juna da ake tattaunawa a kai, tare da jaddada muhimmancin tsagaita wuta a Lebanon.

Mahukuntan Iran sun bayyana cewa tabbatar da tsagaita wuta da kuma mutunta cikakken ikon ƙasar Lebanon na daga cikin muhimman ginshiƙan da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Batun kasancewar sojojin Isra’ila a kudancin Lebanon na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke haifar da ce-ce-ku-ce a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da ƙoƙarin diflomasiyya ke gudana domin rage tashin hankali tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.