An tabbatar da ƙungiyoyin Premier League da za su wakilci Ingila a manyan gasar ƙwallon ƙafa na Turai a kakar wasa mai zuwa.
Ƙungiyoyi biyar sun samu tikitin shiga Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League), wato:
- Arsenal
- Manchester City
- Manchester United
- Aston Villa
- Liverpool
A Gasar Europa League kuwa, ƙungiyoyi uku ne za su fafata, waɗanda suka haɗa da:
- Bournemouth
- Sunderland
- Crystal Palace
Yayin da Brighton & Hove Albion za ta wakilci Ingila a Gasar UEFA Conference League.
Hakan na nufin ƙungiyoyi tara daga Premier League ne za su shiga gasannin Turai daban-daban a kakar wasa mai zuwa, abin da ke nuna ci gaba da ƙarfin da ƙwallon ƙafar Ingila ke da shi a nahiyar Turai.