Ƙungiyar Manchester City na ci gaba da shirye-shiryen sabon kakar wasa yayin da ake rade-radin neman magajin kocinta, Pep Guardiola.
Rahotanni na nuna cewa City na nazarin yiwuwar ɗaukar Enzo Maresca domin jagorantar ƙungiyar, kuma ana sa ran sabon kocin zai fara aiki kafin fara kakar wasa mai zuwa.
Duk wanda zai karɓi ragamar horar da Manchester City, zai fuskanci gwaji mai tsauri tun daga farkon kakar wasa, domin ƙungiyar za ta kara da manyan abokan hamayyarta biyu cikin wasanni shida na farko.
Jadawalin wasannin farko na Manchester City ya haɗa da:
- Bournemouth (Gida)
- Crystal Palace (Waje)
- Coventry City (Gida)
- Manchester United (Waje)
- Sunderland (Gida)
- Liverpool (Waje)
Wasannin da za ta buga da Manchester United da Liverpool ana kallon su a matsayin manyan gwaje-gwaje da za su nuna yadda Manchester City za ta fara kakar wasan.
Magoya bayan ƙungiyar na sa ran ganin yadda sabon koci, idan an naɗa shi, zai tafiyar da ƙungiyar a wannan muhimmin lokaci da ke gab da fara gasar Premier League.