Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Morocco, Achraf Hakimi, zai gurfana a gaban kotu a Faransa bayan masu gabatar da ƙara sun amince da ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin fyade.
Wata mata mai shekara 24 ta zargi ɗan wasan bayan na Paris Saint-Germain da yi mata fyade a gidansa da ke birnin Paris a shekarar 2023.
Ofishin mai gabatar da ƙara a Nanterre, da ke yammacin Paris, ya fara gudanar da bincike kan lamarin tun a watan Maris na shekarar 2023.
A watan Fabrairun 2026, wani alƙali mai bincike ya bayar da umarnin a ci gaba da shari’ar, yayin da rahotanni daga kafofin yaɗa labarai na Faransa suka bayyana cewa Hakimi bai samu nasara ba a ƙoƙarinsa na ganin an yi watsi da ƙarar.
Sai dai Hakimi, mai shekaru 27, ya ci gaba da musanta zarge-zargen da ake yi masa, yana mai cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba.
Duk da batun shari’ar, ana sa ran Hakimi zai jagoranci tawagar ƙasar Morocco a wasansu na gaba a gasar cin kofin duniya.
Tun bayan fara buga wa Morocco wasa a shekarar 2016 yana da shekaru 17, Hakimi ya zama ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan ƙasar, inda ya buga wasanni 97 zuwa yanzu.
Ya kuma taka muhimmiyar rawa a tawagar Morocco da ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniya ta 2022, lokacin da ta zama ƙasa ta farko daga Afirka da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar.