Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar nauyin harin da aka kai a filin jirgin saman Yamai da safiyar Alhamis.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta fitar kuma aka karanta a gidan talabijin na RTN a birnin Niamey, gwamnatin ta yi zargin cewa “masu ɗauke da makamai da Macron ke biya” ne suka kai wani mummunan hari da ya kashe aƙalla sojoji 11 da fararen hula biyu.

Duk da haka, gwamnatin ƙasar ba ta bayar da wata shaidar da za ta tabbatar da wannan zargin ba, kuma Faransa ba ta ce uffan kan batun ba har yanzu.

A cewar sanarwar, maharan waɗanda ake zargi suna sanye da rigunan bama-bamai, kuma sun yi tafiya ne a cikin motocin haya da wasu motocin fararen hula. Sun yi ƙoƙarin afkawa wuraren da ke kusa da filin jirgin Diori Hamani jim kaɗan bayan karfe 6 na safe.

Hukumomin ƙasar sun ce an kashe maharan guda 22, an raunata huɗu, sannan an kama mutane kusan 20.

Rahotanni sun ce an kama wasu tarin makamai da suka haɗa da bindigogin RPG-7, AK-47, bama-bamai, gurneti, kayayyakin sadarwa da dubban alburusai. Jami’ai sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano duk wanda ke da hannu a lamarin.