Bayanan da aka tattara daga WorldAtlas, bisa nazarin alƙaluman Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Eurostat da hukumomin ƙididdiga na ƙasashe daban-daban, sun nuna cewa waɗannan su ne ƙasashen da ake samun ƙarancin saki a duniya:

  1. Indiya – tsakanin 0.01 zuwa 0.1 na saki cikin mutane 1,000.
  2. Sri Lanka0.15 cikin mutane 1,000.
  3. Vietnam0.2 cikin mutane 1,000.
  4. Guatemala0.2 cikin mutane 1,000.
  5. Tajikistan0.3 cikin mutane 1,000.
  6. Bosnia da Herzegovina0.3 cikin mutane 1,000.
  7. Malta0.6 cikin mutane 1,000.
  8. Peru0.6 cikin mutane 1,000.
  9. Chile0.7 cikin mutane 1,000.
  10. Ireland0.7 cikin mutane 1,000.

Me ya sa ake samun ƙarancin saki?

Nazarin ya nuna cewa akwai manyan dalilai uku da suka fi tasiri:

  • Riƙon addini da al'adu: A ƙasashe irin su Indiya, Sri Lanka, Guatemala, Peru da Chile, addini da al'ada suna ƙarfafa dorewar aure tare da rage yawan saki.
  • Tsauraran dokokin saki: Wasu ƙasashe kamar Malta, Ireland da Sri Lanka suna da matakai masu tsauri da tsawon lokaci kafin kotu ta amince da saki.
  • Matsin lambar al'umma: A wasu wurare, ma'aurata kan ci gaba da zaman aure saboda tsoron suka ko tsangwama daga iyali da al'umma.

Muhimmin bayani

Masana sun yi gargaɗin cewa ƙarancin yawan saki ba yana nufin cewa ma'aurata sun fi samun zaman lafiya ba. A wasu lokuta, hakan na iya kasancewa saboda:

  • rashin yin rajistar saki a hukumance,
  • tsauraran dokoki,
  • tsoron cin mutuncin iyali,
  • ko kuma ma'aurata suna ci gaba da zama tare duk da matsaloli saboda matsin lambar al'umma.

A matsakaici, alƙaluman duniya na nuna cewa ana samun kusan saki 1.7 zuwa 1.8 cikin ma'aurata 1,000, yayin da ƙasashen da ke cikin wannan jerin suka yi ƙasa da wannan adadi sosai.