Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Kullen Allah a Najeriya (KACRAN) ta yi Allah wadai da hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina, inda aka kashe mutane, aka ƙone wasu da ransu, tare da yin garkuwa da mutane da dama.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Khalil Mohd Bello, ya sanya wa hannu, KACRAN ta bayyana hare-haren a matsayin rashin imani da kuma babbar barazana ga zaman lafiyar al'umma da wadatar abinci a Najeriya.
Ƙungiyar ta yi kira ga 'yan bindiga da su gaggauta dakatar da kashe-kashe da sace mutane, tare da sakin duk waɗanda suke riƙe da su ba tare da wani sharaɗi ba.
Har ila yau, KACRAN ta roƙi ƙungiyoyin sa-kai da su guji kai hare-hare ko kashe makiyaya marasa laifi, tana mai jaddada cewa ba kowane Bafulatani ba ne ɗan bindiga.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga shugabannin Arewa, ciki har da 'yan siyasa, sarakunan gargajiya, malamai, manoma da makiyaya, da su haɗa kai domin samar da mafita ga matsalar tsaron da ta addabi yankin.
A ƙarshe, KACRAN ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da tsarin zaman lafiya da ƙungiyar ta gabatar, wanda ya haɗa da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki, kare gonaki da hanyoyin kiwo, da kuma nemo hanyoyin kwance damarar 'yan bindiga domin dawo da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.