Yawan maza da ke ɗaukar hutun haihuwa a Japan ya haura kashi 50 cikin 100 a karon farko, lamarin da ke nuna sauyin fahimta da al'adun aiki a ƙasar.
Ma'aikatar Ƙwadago ta Japan ta bayyana cewa adadin ya ƙaru da kusan kashi 10 cikin 100 a shekarar da ta gabata, inda fiye da rabin maza ma'aikata suka amfana da hutun haihuwa domin kula da jariransu.
Tsawon shekaru, gwamnatin Japan na ƙarfafa gwiwar iyaye maza su ɗauki wannan hutu tare da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen tallafi domin inganta daidaito tsakanin aiki da rayuwar iyali.
Manufar waɗannan matakai ita ce sauya tsohuwar al'adar wuraren aiki a Japan, wadda ke sanya maza cikin matsin lamba su yi aiki na tsawon sa'o'i, tare da tsoron cewa ɗaukar hutun haihuwa na iya hana su samun ƙarin girma ko ci gaba a aikinsu.