Sanata Rufai Hanga, mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NDC, jam'iyyar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ke jagoranta.
A cikin wasiƙar murabus da ya aike wa shugabannin jam'iyyar ranar 3 ga Agustan 2026, Sanata Hanga ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar ne bayan dogon nazari da tunani kan makomarsa ta siyasa.
Ya kuma gode wa shugabannin jam'iyyar da mambobinta a mazabar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano bisa goyon baya, haɗin kai da kuma damar da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.
Sanatan ya ce ya miƙa katin shaidar kasancewarsa ɗan jam'iyyar tare da neman a cire sunansa daga rajistar mambobin NDC a matakin mazaba.
A ƙarshe, Sanata Rufai Hanga ya yi wa jam'iyyar NDC da dukkan mambobinta da magoya bayanta fatan alheri a ci gaba da harkokinsu na siyasa.