Rundunar ’Yansandan Nijeriya, tare da haɗin gwiwar Hukumar ’Yansandan Ƙasa da Ƙasa (INTERPOL), ta tasa ƙeyar wani ɗan ƙasar China mai suna Cai Jinlian (42) zuwa ƙasarsa domin fuskantar tuhuma kan zargin safarar namun daji masu fuskantar barazanar ɓacewa.

Ana zargin Cai Jinlian da safarar kimanin tan 12 na kwanson dabbar ɗan-kunya (pangolin scales) daga Nijeriya zuwa China a jigila biyu tsakanin Nuwamban 2018 da Afrilun 2019.

Binciken da Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Kwastam ta Wenzhou ta gudanar ya gano laifin, inda aka gurfanar da wasu abokan aikinsa biyu, waɗanda kotu ta yanke musu hukuncin ɗaurin fiye da shekara 14 a watan Disamban 2020.

Bayan ya tsere daga China zuwa Masar a shekarar 2019, INTERPOL ta sanya sunansa cikin jerin waɗanda ake nema ruwa a jallo. Daga baya bayanan sirri suka nuna cewa ya koma Nijeriya a kusan shekarar 2023, inda yake zirga-zirga tsakanin jihohin Delta da Filato.

Jami'an INTERPOL da ke Abuja sun kama shi a ranar 18 ga Yulin 2026, kafin daga bisani a tasa ƙeyarsa zuwa Shanghai a ranar 29 ga Yulin 2026, domin ya fuskanci shari'a a China.

Babban Sufeton ’Yansandan Nijeriya, Olutunji Rilwan Disu, ya yaba da ƙwarewa da jajircewar jami'an INTERPOL wajen gudanar da aikin, tare da jaddada kudurin rundunar na ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro na ƙasa da ƙasa wajen yaƙi da manyan laifukan ƙetare da kuma kare namun daji masu fuskantar barazanar ɓacewa.