Turkiyya na ƙara faɗaɗa masana'antar ƙera jiragen ruwa, yayin da take shirin taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Nijeriya cimma burinta na ƙera jiragen ruwa a cikin gida, sabunta tsofaffin jiragen ruwa da bunƙasa tattalin arzikin teku (Blue Economy).
Wannan haɗin gwiwa ya biyo bayan ziyarar aiki da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kai Turkiyya a farkon wannan shekara, inda alaƙar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara ƙarfi, tare da karkata daga cinikayya zuwa haɗin gwiwar masana'antu na dogon lokaci.
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na son kamfanonin ƙera jiragen ruwa na Turkiyya su zama abokan hulɗa na dindindin wajen gina ƙarfin ƙasar na ƙera jiragen ruwa a cikin gida, musayar fasaha da bunƙasa masana'antar ruwa.
Majalisar Kasuwanci ta Nijeriya da Turkiyya tare da dandalin DAMISE na jagorantar tattaunawa kan haɗin gwiwa a fannoni da suka haɗa da ƙera jiragen ruwa, gyaransu, musayar fasaha da kuma inganta sufurin cikin ruwa.
Ma'aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku ta Nijeriya ta kuma buƙaci kamfanonin Turkiyya su ɗauki Nijeriya a matsayin cibiyar ƙera jiragen ruwa ga nahiyar Afirka, musamman saboda damar kasuwancin da Yankin Ciniki Marar Shinge na Nahiyar Afirka (AfCFTA) ke bayarwa.
Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Cikin Gida ta Nijeriya (NIWA) ta gayyaci kamfanonin Turkiyya su shiga haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu wajen ƙera jiragen ruwa da gina tashoshin ruwa a hanyoyin ruwa masu tsawon kusan kilomita 3,000 da ake iya zirga-zirga.
Alƙaluma sun nuna cewa darajar fitar da jiragen ruwa daga Turkiyya ta haura daga dala miliyan 900 a shekarar 2018 zuwa dala biliyan 3 a shekarar 2025, lamarin da ya sanya ƙasar cikin manyan ƙasashe goma na duniya wajen ƙera jiragen ruwa.
A lokaci guda kuma, kuɗin da Nijeriya ke kashewa wajen shigo da jiragen ruwa ya ragu daga dala biliyan 3.4 zuwa kusan dala miliyan 500, sakamakon ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida.
A halin yanzu, Turkiyya na da masana'antun ƙera jiragen ruwa 85, jiragen ruwa sama da 2,270, da kuma cibiyoyin horas da ƙwararru a fannin harkokin ruwa, abin da ke ƙara tabbatar da ƙwarewarta a wannan fanni.
Ana sa ran haɗin gwiwar zai mayar da hankali kan ƙera jiragen kamun kifi, jiragen tallafa wa ayyukan teku, cibiyoyin gyaran jiragen ruwa, bunƙasa hanyoyin sufurin cikin gida, da kuma shirye-shiryen rage gurɓatar muhalli, horas da ƙwararrun ma'aikata da samar da hanyoyin samun kuɗaɗen zuba jari.
An tsara gudanar da ƙarin tarurruka a 30 ga Yuli da kuma 5 ga Agusta domin daidaita bukatun Nijeriya da ƙwarewar kamfanonin Turkiyya, yayin da ake sa ran a ƙarshe za a bayyana Tsarin Haɗin Gwiwar Harkokin Ruwa tsakanin Turkiyya da Nijeriya na shekarar 2027.