Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin tawaga daga Ministry of Finance Incorporated (MOFI) da kamfanin Mota-Engil Nigeria gabanin bikin ƙaddamar da aikin gina Layin Dogon Jirgin Ƙasa na Kano (Kano Light Rail Project), wanda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da aiwatar da shi.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Dr. Armstrong Ume Takang na MOFI da Shugaban Kamfanin Mota-Engil Nigeria, Mista Kola Karim, ta gana da Gwamna Yusuf a Masaukin Gwamnan Jihar Kano da ke Asokoro, Abuja, domin yi masa bayani kan matakin shirye-shiryen fara aikin.
Aikin Layin Dogon Jirgin Ƙasa na Kano, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi kan kuɗin kwangilar da ya kai Naira tiriliyan 1.05, ana sa ran zai sauya tsarin sufurin cikin birnin Kano, inganta haɗin kai tsakanin sassa daban-daban na birnin, rage cunkoson ababen hawa, tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi maraba da tawagar, tare da jaddada aniyar Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da yin aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya da kamfanonin da ke aiwatar da aikin domin tabbatar da nasarar wannan muhimmin aikin raya ƙasa.
Ya bayyana aikin layin dogon jirgin ƙasan a matsayin wata muhimmiyar zuba jari da za ta ƙara tabbatar da matsayin Kano a matsayin cibiyar kasuwanci ta Arewacin Nijeriya, tare da samar wa al'umma ingantaccen tsarin sufuri na zamani, mai aminci da inganci.
Gwamnan ya kuma bayyana matuƙar godiyarsa ga Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunonin Sojin Nijeriya, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, bisa amincewa da aiwatar da wannan gagarumin aiki a jihar Kano.
Haka kuma, ya miƙa godiya ta musamman ga Hon. Abubakar Kabir Bichi, Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, bisa irin gudunmawar da ya bayar ta fuskar tallafin majalisa domin ganin aikin ya samu amincewa.