Kocin Tottenham Hotspur, Roberto De Zerbi, ya bayyana cewa yana son ɗan wasan baya Djed Spence ya ci gaba da zama a ƙungiyar, duk da jita-jitar da ke alaƙanta shi da komawa Inter Milan ko Everton.
Spence mai shekara 25, wanda ya sabunta kwantiraginsa na dogon lokaci da Tottenham a bara, na cikin 'yan wasan da ake hasashen za su sauya sheƙa a wannan kasuwar cinikin 'yan wasa.
Sai dai De Zerbi ya ce yana kallon Spence a matsayin muhimmin ɓangare na shirinsa na gina ƙungiyar, duk da cewa yana sa ran ƙara wasu sababbin 'yan wasa kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa.
Ya zuwa yanzu, Tottenham ta kashe kusan fam miliyan 237 wajen ƙarfafa ƙungiyar domin tunkarar kakar Premier League ta 2026/2027, bayan ta tsallake rijiya da baya a kakar da ta gabata.
Spence ya fara wasa a wasanni 23 cikin 30 da ya buga a kakar bara, duk da cewa Tottenham ta kammala gasar a matsayi na 17.
A halin yanzu, Pedro Porro na Spain ya mamaye gurbin ɗan wasan baya na dama, lamarin da ya sa Spence ya fi taka leda a matsayin ɗan wasan baya na hagu a lokutan baya-bayan nan.