Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya aike da wasiƙa ga hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe mambobi 211, inda ya sanar da cewa za su iya samun dala miliyan 40 idan suka amince da wani sabon tsari mai cike da ce-ce-ku-ce kan sayar da wani ɓangare na kasuwancin gasar Kofin Duniya.
A cewar wasiƙar, Infantino ya ba hukumomin ƙwallon ƙafa wa'adin 19 ga Satumba su bayyana amincewarsu da shirin. Idan suka amince cikin wa'adin, za a fara biyansu dala miliyan 20 nan da 1 ga Janairun 2027, yayin da za a biya sauran kuɗaɗen daga baya.
FIFA ta bayyana cewa sabon tsarin zai samar da wani kamfani na kasuwanci da zai riƙa gudanar da wasu muhimman harkokin kasuwancin gasar Kofin Duniya, tare da bai wa masu zuba jari na waje damar mallakar hannun jari.
Sai dai cikin ƙasa da sa'o'i 24 bayan bayyana shirin, an fara fuskantar suka daga hukumomin ƙwallon ƙafa na Turai, Asiya da Arewacin Amurka, waɗanda ke nuna damuwa kan tasirin shirin ga makomar gasar.
Rahotanni sun kuma ce Infantino bai tattauna da dukkan mataimakansa takwas kafin gabatar da wannan tsari ba, duk da hasashen cewa sabon tsarin zai iya samar wa FIFA da kuɗaɗen shiga da suka kai dala biliyan 10.
BBC ta ce ta samu kwafin wasiƙar mai shafuka biyar da Infantino ya sanya wa hannu, wadda ta yi cikakken bayani kan sabon shirin da kuma fa'idodin da FIFA ke ganin zai haifar ga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya.