Jami'an tsaron Najeriya sun kashe 'yan bindiga uku tare da ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a wani samame da aka gudanar a Jihar Kwara.
An gudanar da aikin ne ta haɗin gwiwar dakarun Rundunar Sojin Najeriya, jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), dakarun tsaron gandun daji, mafarauta da kuma 'yan sa-kai a yankunan Obbo-Aiyegunle, Ejiu-Ora da Osi da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar Kwara, kusa da iyakar Jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da mutanen ne daga al'ummar Eju, kuma masu garkuwar na kan hanyarsu ta bi ta cikin daji zuwa Jihar Neja lokacin da jami'an tsaro suka kai samamen ceto.
A yayin artabun, jami'an tsaron sun kashe mutum uku da ake zargin 'yan bindiga ne, tare da kubutar da dukkan mutanen tara da aka sace.
A cikin 'yan watannin nan, Jihar Kwara na fuskantar ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka kan fararen hula da jami'an tsaro.
A wani mataki na ƙarfafa tsaro, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabon bataliyar sojoji a jihar a ranar 22 ga Yuli, domin ƙarfafa yaƙi da 'yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, ciki har da ƙungiyar Mahmuda, wadda gwamnatin tarayya ta bayyana a matsayin wani reshe na Boko Haram.