Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari a wata kotun shari'a da ke ƙauyen Gwarjo, a Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina, inda Alƙali Mohammed Muktar ya tsira bayan ya tsere ta taga kafin maharan su kutsa cikin kotun.

Rahotanni sun ce mazauna yankin sun ga maharan suna tunkarar kotun a ranar 29 ga Yuli, lamarin da ya sa alƙalin ya fice cikin gaggawa ta taga kafin su isa.

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun shiga kotun suna harbe-harbe tare da tambayar inda alƙalin yake. A cewarsa, wani direban babur mai ɗaukar fasinja (acaba) ne ya taimaka wa Alƙali Muktar ya tsere daga yankin kafin maharan su same shi.

Shaidu sun kuma ce maharan sun yi barazanar kashe alƙalin idan ya sake komawa kotun domin ci gaba da sauraron shari'o'i.

Mazauna yankin na zargin cewa maharan sun kai harin ne da nufin kashe Alƙali Mohammed Muktar ko kuma yin garkuwa da shi domin neman kuɗin fansa.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.