Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ɗaya daga cikin hanyoyin da ake amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur shi ne tallafa wa ilimin ɗalibai a faɗin Najeriya.


Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Harkokin Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya ce gwamnati na ɗaukar nauyin wasu shirye-shiryen tallafin karatu domin rage wa ɗalibai da iyayensu nauyin kuɗin karatu.


A cewarsa, kuɗaɗen da aka samu daga sauye-sauyen da aka yi kan tsarin tallafin man fetur ba su tsaya ga ayyukan gine-gine kaɗai ba, har ila yau ana karkatar da wani ɓangare daga cikinsu zuwa shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al’umma, ciki har da fannin ilimi.


Ya ce:

“Ɗaya daga cikin hanyoyin da kuɗaɗen tallafin man fetur ke tafiya akwai tallafin makaranta da gwamnati ke ɗauka ga kowane ɗalibi a Najeriya.”


Kalaman na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tambayoyi daga jama’a kan yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur.


Gwamnatin Tarayya ta sha bayyana cewa tana mayar da kuɗaɗen zuwa muhimman fannoni kamar ilimi, lafiya, samar da ababen more rayuwa da kuma shirye-shiryen tallafawa rayuwar ’yan Najeriya.