Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Kudu maso Gabas na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a Taron Tsaro na Yankin Kudu maso Gabas da aka gudanar a Umuahia, babban birnin Jihar Abiya.
Ya ce samar da tsaro mai ɗorewa ba zai yiwu ba sai da haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin tarayya da jihohi, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da kuma al'umma baki ɗaya.
Mohammed Idris ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ƙarfafa hukumomin tsaro ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki, bunƙasa tattara bayanan sirri da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Abiya, Dakta Alex Otti, tare da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) da sauran wakilan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sun jaddada cewa magance matsalolin tsaro na buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati, jami'an tsaro da al'umma.
Sun kuma yi kira da a aiwatar da gyare-gyaren dokoki, samar wa matasa damar tattalin arziki, inganta musayar bayanan sirri da kuma ƙarfafa amincewa tsakanin jama'a da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a yankin Kudu maso Gabas da Nijeriya baki ɗaya.