Hukumar Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yi kira ga wanzamai da su ƙara zamanantar da sana'arsu tare da kawar da duk wasu dabi'u marasa kyau da ke bata martabar aikin, tana mai jaddada cewa addinin Musulunci ya ba da muhimmanci ga kare lafiya, rayuka da dukiyoyin al'umma.
Kwamishina na Biyu na Hukumar, Sheikh Ali Ɗanabba, ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarkin Askar Kano, Alhaji Muhammad Yunusa Na Bango, a wata ziyarar aiki da aka gudanar domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da ci gaban al'umma.
A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun tattauna kan hanyoyin magance matsalolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, faɗan daba, rashin tsaro, da kuma yadda za a inganta harkar wanzanci tare da daidaita tallace-tallacen magungunan gargajiya domin su kasance cikin tsarin doka da koyarwar addinin Musulunci.
Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma buƙaci Sarakunan Askar da su ƙara taka rawa wajen yaƙi da ayyukan ta'addanci da suka haɗa da ƙwacen waya, faɗan daba da dillancin miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, ya yi kira gare su da su wayar da kan masu sana'ar magungunan gargajiya su guji amfani da kalamai ko hanyoyin talla da ke saɓa wa ɗabi'a da tarbiyya.
A nasa jawabin, Sarkin Askar Kano, Alhaji Muhammad Yunusa Na Bango, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne bisa gayyatar Hukumar Shari'ar Musulunci, inda ya ce sun cimma matsayar ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumar domin inganta tsaro, bunƙasa sana'o'i da kuma tallafa wa ci gaban Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.